Ƙungiyar dattawan arewacin Najeriya, Arewa Consultative Forum, ta yi kira ga gwamnatin tararraya da ta cire takunkuman da ta sanyawa Nijar, sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar.
A makon jiya ƙungiyar ta ACF ta soki batun aiki da ƙarfin soji da kungiyar Ecowas din ta ce za ta yi idan sauran matakai sun gagara.
Dattawan sun kuma yaba wa ƴan majalisar dokokin Najeriyar da suka yi watsi da maganar aikewa da karfin sojin.
A wa ni labarin, rahotanni daga jihar sokoto na nuni da cewar, Takunkumin da ƙungiyar ta Ecowas ta ƙaƙaba wa Nijar ya haifar da tashin farashin kayan abinci a kasar, wanda kuma ya shafi wasu jihohi a nan gida Najeria.
Mazauna jihar Sokoto da ke maƙwabta da Nijar sun koka kan yadda farashin shinkafa ya ke hauhawa.