A Yau Juma’a, Kungiyar Editoci ke gabatar da babban taro don zaban sababbin Shugabanni da za su jagoranci Kungiyar na shekaru biyu.
Taron wanda ake gudanarwa a Owerri ta Jihar Imo, zai samu halartar Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shattima wanda zai yi bikin bude shi, yayin da Gwamna jihar Imo Hope Uzodimma zai kasance a matsayin Mai masaukin baki.
Kimanin Editoci 400 – 500 ake sa ran za su halarci taron don kada kuri’a.
Yan takara 26 wanda kwamitin zabe na Kungiyar ya tantance za su fafata.
Daga ciki a kwai Yan takara 2 daga Jihar Kano wanda suka hada da Muhammad Sanusi Jibrin da Umoru Ibrahim.
A yammacin yau, a ke sa ran samun sakamakon zaben Kuma za’a rantsar da sababbin Shugabannin da aka zaba.