Kungiyar Editocin Najeriya ta zabi Eze Anaba na Jaridar Vanguard a matsayin Shugaba.
Eze ya Samu kuri’u 250 akan abokin takararsa Bolaji Adebiyi na This Day wandà ya tsira da kuri’u 81.
Sauran wadan aka zàba sun hada da Hussaina Akila Banshika ta Gidan Radiyo Tarayya da ke Abuja a Matsayin mataimakiyar shugaba, da Umoru Ibrahim na Jaridar Triumph da ke aka zaba matsayin Mataimakin Shugaba shiyyar Arewa.
Sauran su ne Iyobosa Uwugiaren a matsayin Sakatare, sai Steve Nwosu a matsayin ma’ajin kungiya.
An Kuma zabi Tsohon Darektan sashen Labarai da al’amuran yau da kullum na Gidan Talabiji na Abubakar Rimi da ke Kano Muhammad Sanusi Jibrin matsayin memba Mai wakiltar shiyar Arewa.
Zaben Wanda aka gudanar a Otel din Rockview da ke Owerri Jihar Imo, ya samu halartar Editoci gidajen Jaridun kasar nan da na Gidajen Radiyo da Talabijin sama da 500 daga jihohin kasan nan.