Kungiyar kwadago ta kasa, NLC, ta yi barazanar tafiya yajin aiki a kasa bakidaya, idan aka samu ƙarin farashin man fetur daga 617 da ake siyarwa a gidajen man ƙasar nan.
Shugaban kungiyar ta kasa , Joe Ajaero, ya bayyana haka a yayin wata tattaunawa da kungiyar ta yi.
Ya kuma gargadi gwamnatin tarayya kan yin shakulatun-bangaro da koken da kungiyar ta shigar gabanta.
Rahotanni na nuni da cewa tuni aka fara hasashen cewa farashin man fetur zai koma 680 ko 720 nan ba da dadewa ba matukar dalar ta cigaba da tashi zuwa 910 ko 950.
A kwanakin bayan nan ne dai kungiyar ta janye yajin aikinta bayan ganawa da ta yi da shugaba Bola Ahmad Tinubu.