Kungiyar kwadago ta Najeriya ta NLC ta ce za ta fara yajin aiki na gama-gari daga ranar Laraba, 7 ga watan nan na Yuni.
Shugaban kungiyar Joe Ajaero shi ne ya sanar da haka, bayan wani taron gaggawa da shugabannin kungiyar suka yi yau a Abuja.
Daman a yau ne shugabannin suka kira wannan taro domin tattaunawa da bayyana matakin da za su dauka bayan da sabon shugaban kasar ya furta cewa kasar ta janye tallafin mai.
Wannan sanarwa ta shugaban ta janyo tashin farashin man a sassan kasar, inda aka rinka samun dogayen layukan ababan hawa a gidan mai.