Kungiyar Likitocin Masu Neman Kwarewa da ke aiki a asibitocin gwamnati sun bai wa gwamnatin kasar nan wa’adin mako biyu da ta cika musu alkawuran da ta daukar musu game da jarjejeniyar da suka cimma a baya.
Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin da ta shude ta shugaba Muhammad Buhari ta ba su tabbacin magance matsalolinsu bayan tsuduma yajin aikin gargadi da kungiyar ta yi na kwanaki biyar a watan Mayun wannan shekara.
A cikin wata sanarwa da kungiyar likitocin Najeriya NARD ta fitar, ta ce ta yi imanin cewa wa’adin mako biyu ya isa hukumomi su magance mata matsalolinta.
A cewar kungiyar sun ji shiru ne tun bayan da sabon shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya ɗare karagar mulkin, duk kuwa da masaniya da yake da ita na waccan yarjejeniya da kungiyar ta kulla da tsohon shugaban kasa Buhari.
Ƙungiyar ta yi gargadin cewa matukar aka gaza biya mata bukatunta zuwa ranar 19 ga watan Yulin da muke ciki, “Fannin kiwon lafiyar kasar zai sake shiga wani hali”.
Rashin isassun kuɗaɗe, da rashin isassun kayan aiki da karancin albashin ma’aikatan kiwon lafiya ana ganin su ne dalilan da ke sanya kwararrun likitoci da dama na neman ayyuka a ƙasashen waje a maimakon zama a kasar nan.