Daya daga cikin manyan kungiyoyin man fetur da iskar gas a Najeriya za ta shiga yajin aikin da za a fara daga ranar 3 ga watan Oktoba a fadin kasar domin nuna adawa da manufofin gwamnati da ke janyo wa ‘yan Najeriya kuncin rayuwa da tabarbarewar tattalin arziki, in ji shugabannin kungiyoyin.
Kungiyar ma’aikatan man fetur da iskar gas ta Najeriya (NUPENG) ta umurci mambobinta da su tabbatar da bin ka’idar yajin aikin sai-baba-ta-gani da manyan kungiyoyin kwadago na kasa suka kira.
Kungiyar ta NUPENG tana wakiltar dimbin ma’aikata ne a sassan mai da iskar gas, wadanda suka hada da ma’aikatan mai, da direbobin tankokin mai da masu aikin famfo a gidajen mai, kuma matakin da ta dauka na shiga yajin aikin wani gagarumin ci gaba ne na takaddamar kungiyoyin da gwamnati.