Kwamishinan ƴan sandan jahar Kano CP Muhammad Usaini Gumel ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan masu amfani da rashin lafiyar A.A. Rufa’i wajen tunzura da yaɗa shi a safukan sada zumunta.
Wannan dai na zuwa bayan da lauyan A.A. Rufa’i da aka fi sani da Bill gate, Barista Badamasi Sulaiman Gandu, ya shigar da koken yadda wasu matasa ke amfani da shafukan sada zumunta suna ƙara tunzura shi da tsokanarsa har ma ya yi zargin cewa ana sanya masa ƙwaya a lemon kwalba dan ya sha ya ƙara tunzura shi.
Manema labarai sun rawaito cewa mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jahar Kano SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da karɓar korafin da kuma umarnin da kwamishinan ƴan sandan jahar CP Muhammad Gumel ya bayar na gayyato wasu daga cikin mutanen da ake zargi dan faɗaɗa bincike kan zargin.
SP Kiyawa, ya ce rundunar ba za ta zura ido ba, wasu na aikata abubuwan da ba su dace ba, wanda ya zama wajibi a ɗauki mataki kan lamarin domin kowanne ɗan ƙasa yana da yanci da bai kamata a ci zarafinsa ba ta kowacce hanya.