Home » Kwamishinan ‘yan sandan Kano ya ja hankalin al’umma kan muhimmancin magance matsalar Daba

Kwamishinan ‘yan sandan Kano ya ja hankalin al’umma kan muhimmancin magance matsalar Daba

by Yasir Adamu
0 comment
Kwamishinan 'yan sandan Kano ya ja hankalin al'umma kan muhimmancin magance matsalar Daba

Hukumar Yan Sandar Jihar Kano ta ce, idan akayi sake da harkar a daba a jahar, to zata fi irin matsalar da aka samu a yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya.

Kwamishinan Yan Sanda na Jahar, Muhammad Husaini Gumel ne ya bayyana haka yayi da ya ziyarci Dutsen Dala dake kwarayar burnnin jahar kano.

Dutsen Dala dake da tsahon tarihi a jahar kano, Wasu masanan na ganin cewa tarihin kano bazai taba kammaluwa sai an hada da tarihin dutsen na dala.


Sai dai a yanzu Dutsen ya zama barazana, kuma mafaka ga masu aikata laifuka musamman yan daba.


Hakan ta sanya kwamishinan jahar kano Muhammad Husaini Gumel ya ziyarci wannan dutse don gane ma idon sa yanayin wannan dutse da kuma yadda masu laifin ke amfani dashi a matsayin mafaka


Cp Muhammad Husaini Gumel ya bayyana irin matakin da suka dauka na gayyatar wasu shuwagabanin yan daba zuwar shelkwatar hukumar tare tattaunawa dasu sanan kuma wadan da suka ki kwamshinan yayi umarni ga yan sanda da sauran jami’ an tsaro da su kamo su don su fuskanci hukunci.


Shugabbanin da manya a unguwar ta dala sun bayyana gamsuwar da shirin na kwamshinan yan sanda da kuma godiyar gare shi na kawo musu dauki.


Kwamishinan ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da su cigaba da bada hadin kai ga yansanda da saura jami’an tsaro wajen dakile masu aikata laifi a ckin su.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi