Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano ta sanya tukuicin naira dubu ɗari uku ga duk wanda ya ba wa hukumar bayani game da wasu ‘yan daba da take nema ruwa a jallo.
Wannan na zuwa ne a wani ɓangare na cigaba da yaƙi da ayyukan daba da ƙwacen waya a jihar nan wanda kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano ya sha alwashin kawo ƙarshensa.