An gudanar da sallar Idin ne da misalin ƙarfe 8:30 na safe wanda limamin Kano Farfesa Sani Zahraddeen ya jagora.
Farfesa Sani Zahraddeen
Mai martaba sarkin Kano, Alh. Aminu Ado Bayero, ya halarcin sallar tare da hakimansa da sauran manyan hadimansa.
Mai martaba sarkin Kano, Alh. Aminu Ado Bayero
Haka shi ma mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, na cikin manyan jami’an gwamnatin jihar Kano da suka halarci salla a masallacin.
Sannan akwai mutane kamar sanata Kabiru Gaya da shugaban Hukumar Karota, Baffa Babba Dan’Agundi da Ali Baba a Gama Lafiya da sauransu.