A yayin da ake cigaba da dambarwar batun cire tallafin mai da gwamnatin Tarayya ta yi, sai ga masu hayar motocin bas a jihar Ikko na nuna goyon bayansu game da cire tallafin man fetur da gwamnatin ta yi.
Matuƙa motocin hayar bas ɗin sun bayyana hakan ne a yayin wani zaman tattaunawa a ƙarƙashin jagorancin ma’aikatar garejojin mota da wuraren shan iska.
Mataimakin shugaban ma’aikatar, Alhaji Sulaimon Ojora, ya yaba wa direbobin bisa fahimtar manufofin gwamnati da kuma tabbacin da suka bayar na ba za su ƙara kudin hayar motocin ga fasinjojinsu ba.
Sannan Ojora ya ce, sun kira masu sana’ar ne domin ka da wasu daga cikin mambobinsu su yi amfani da wannan dama wajen gallaza wa jam’a ta hanyar ƙara musu kudin mota.
Ya kuma tabbatar da cewa an samar da kwamiti mai mutane bakwai wanda zai sa ido game da kuɗin da ake karɓa a hannun fasinjoji.
A ƙarshe ya roƙi sauran masu hawar motoci da ke sauran jihohin ƙasar nan da su yi ko yi da takwarorinsu na jihar Legas ta hanyar kaucewa ƙara kudin abin hawa.