Allahu Akbar!
Allah ya yi wa Magajin Rafin Hadeja Alhaji Mohammadu Babandede Sarkiki rasuwa.
Marigayin mahaifi ne ga mahaifi ne ga shugaban gidan rediyo da talabijin na Muhasa, Muhammad Babandede, kuma tsohon shugaban hukumar shigi da fici ta ƙasa.
Magajin Rafin Hadejia Alhaji Mohammadu Babandede Sarkiki ya rasu ne a jiya, Lahadi da daddare a ƙasar Egypt wato Masar.
Za a sanar da rana da lokacin jana’izarsa da zarar gawarsa ta iso gida daga birnin AlƘahira.
Ɗaukacin ma’aikatan Muhasa na miƙa ta’aziyarsu ga mai wannan gida Muhammad Babandede da duka ƴan uwansa
Muna addu’ar Allah Ya ji ƙansa, Ya rahamshe shi, Ya gafarta masa.
Ƴaƴa da jikoki da ƴan uwa da abokan arziki Allah Ya ba da haƙurin rashin sa.
Allah Ya kyautata namu ƙarshen Ya haɗa mu da su a Aljanna. Amin.