Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya karyata rahoton da wasu kafafen yada labarai suka wallafa cewa, Ya ce jami’an tsaro na guje wa ‘yan bindiga, amma suna cin zarafin mutanen da ‘yan bindigar suka sace.
Sanarwar ta ce, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, bai furta cewa jami’in tsaro na guje wa ‘yan bindiga, amma suna cin zarafin mutanen da ‘yan bindigar suka sace ba.
Sanarwar ta ƙara da cewa, bayanin da Sultan ya yi shi ne, idan ‘yan bindiga suka kai hari cikin al’umma suka kashe mutane tare da kone gidaje, ba a daukar wani mataki akai.