Tsohuwar Shugabar Kotun Daukaka Kara ta Najeriya Mai Shari’a Zainab Bulkachuwa ta musanta kalaman da mai gidanta ya yi na cewa ya yi amfani da damarsa, wajen nema wa abokan siyasarsa Sanatoci alfarma lokacin da take aiki a matsayin alkaliya.
Cikin wata gajeruwar sanarwa, Mai Shari’a Zainab ta ce cikin tsawon lokacin da ta kwashe tana aiki ba ta taba yi wa wani mutum amfarma ba a duk tsawon shekarun da ta kwashe tana aiki a zaman mai shari’a.
Tsohuwar shugabar kotun daukaka karar, wacce ta shafe shekaru arba’in tana aikin shari’a, ta ce masu shari’a a karkashin jagorancinta za su iya bayar da shaida a kan cewa ba ta taba tsoma baki ga ‘yancin kansu ba.
Ta bayyana cewa; “An jawo hankalina kan bidiyon abin da mijina, Sanata Adamu M. Bulkachuwa ya fada. Ina so in bayyana a fili cewa ban taba saba rantsuwar da na yi na kin nuna fifiko ga wani bangare da ya gurfana a gabana ba cikin shekaru 40 da na kwashe ina hidimta wa kasata ba’’.