Home » Majalisar dattijai ta tantance Wike, Badaru da wasu ministoci cikin 28 dake gabanta

Majalisar dattijai ta tantance Wike, Badaru da wasu ministoci cikin 28 dake gabanta

by Anas Dansalma
0 comment
Majalisar dattijai ta tantance Wike, Badaru da wasu ministoci cikin 28 dake gabanta

A cigaba da tantance ministocin da majalisar Dattijai ke yi, rohotanni sun tabbatar da cewa majalisar ta tantance wasu daga cikin sunayen da aka gabatar mata.

Wasu daga cikin waɗanda majalisar ta tantance izuwa yanzu sun haɗa da:

Tsohon gwamnan jihar Jigawa Badaru Abubakar wanda shugaban Majlisar ya ce yana da kyakkyawar alaƙa tsakaninsa da tsohon gwamnan saboda haka ya umarce shi ya wuce abins a matsayin wanda aka tantance.

Sai kuma tsohon gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike wanda shi majalisar ta domin kuwa bai fuskanci wasu tsauraran tambayoyi ba daga Majalisar, inda shugaban majalisar Godswill Akpabio ya buƙaci ya risina wa majalisa, ya wuce.

Ita ma Nkeiruka Onyejocha rusunawa kawai ta yi.

 Sanata Nkeiruka Onyejocha ta fito daga Jihar Abiya da ke kudu maso gabashin Najeriya.

Sanata ɗaya ne daga jiharta ta Abiya ya yi magana a kanta – shi ma yabonta ya yi a matsayinta na lauya, tsohuwar ‘yar majalisa, tsohuwar kwamashina.

Shugaban Majalisa Godswill Akpabio ya nemi ta rusuna kawai ta wuce ba tare da wasu tambayoyi ba – saboda ‘yar uwarsu ce tshohuwar ‘yar majalisa.

Nkeiruka ta je Majalisa ne tun daga 2003 har zuwa zaɓen 2023, inda ta yi rashin nasara.

Sai dai akwai waɗanda aka samu taƙaddama a yayin tantance su da suka haɗa da:

Umarci Bello Goronyo wanda majalisar ta bukaci ya gabatar da sauran takardun karatunsa.

Wasu daga cikin Sanatocin sun yi tambaya ga Hon Bello Goronyo, kan gudumuwar da zai bayar wajen magance matsalar tsaro da yankin da ya fito ke fuskanta.

Sannan akwai  umarci Yusuf Tuggar wanda shugaban Majalisar Dattawa ya buƙace shi da ya gababatar da takardar haihuwarsa da sauran takardun makarantarsa gaban majalisar saboda rashin kawo su da ya yi nan take.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi