A zaman da ta gudanar a yau Litinin majalisar dokokin jihar Kano, ta amince da ƙarin kasafin kudin shekarar 2023, wanda hakan ke nuna wani gagarumin cigaba ga ayyukan raya jihar.
Karin kasafin kudin ya haura sama da Naira miliyan dubu 58, daga ciki an ware kashi 92 cikin 100 don aiwatar da ayyukan raya ƙasa da walwalar al’ummar jihar yayin da aka ware ragowar kashi 8 domin gudanar da ayyuka masu bijirowa na yau da kullum.
Manufar wannan ƙarin kasafin kudin ita ce, samar da tsarin kudin da ya dace don aiwatar da wasu ayyuka masu tasiri a fadin jihar. Gwamnan Abba Kabir Yusuf ne ya mika kudurin kasafin kudin ga majalisar domin ta duba tare da amincewa tun kwanakin baya.