Majalisar dokokin kasar Jamhuriyar Nijar, ta kaddamar da sabon taken kasar wanda kasar ta samar domin maye gurbin wanda ta gada daga Faransa.
Illahirin ‘yan majalisar dokokin kasar na bangaren masu mulki da ‘yan adawa ne suka kada kuri’ar amincewa da sabon taken bayan yin gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin kasar.
Sabon taken wanda ke rubuce zai dauki mutum tsawon minti daya ne da sakonni 41 wajen karantawa.
Assoumana Malam Issa tsohon ministan raya al’adu kuma mamba a kwamitin rubuta sabon taken kasar ta Jamhuriyar Nijar ya bayyana wasu daga cikin sakonni da sabon taken ke isarwa.
Duk da yake cewa ‘yan majalisar dokokin adawa sun kada kuri’ar amincewa da sabon taken kasar ta Jamhuriyar Nijar, sai dai Soumana Sanda na jam’iyyar adawa ta Lumana Afirka, ya gargadi gwamnati kan cewa sauya taken ba wani sauyin da zai haifar ga kasar matsawar gwamnatin ba ta sauya hali ba.
‘Yan kasa da dama ne dai suka hallara a zauran majalisar dokokin domin halartar mahawara da kuma kaddamar da sabon taken kasar.
Bayan kaddamar da sabon taken a gaban majalisar dokoki, ba za a soma aiki da shi ba a bainar jama’a sai bayan shugaban kasa ya sanya hannu kan sabuwar dokar da ta haifar da sabon taken da ake sa ran zai yi nan da makonni biyu masu zuwa.