Majalisar Wakilan ƙasar nan ta buƙaci a ƙara yawan kuɗin da aka ware domin ba dalibai rance, wanda a baya aka ware wa miliyan dubu 10.
Majalisar ta bijiro da hakan ne bayan da ta ƙi amincewa da bukatar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta kashe Naira miliyan dubu 5 daga cikin kasafin kuɗi tiriliyan 2 da biliyan 17 wajen sayen jirgin ruwa.
Matakin ƴan majalisar ba zai rasa nasaba da koke-koken da ƴan Najeriya suka riƙa yi ba tun bayan bullar labarin sayen jirgin ruwan shugaban kasar, a daidai lokacin da suke cikin kuncin rayuwa.
Shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar, Abubakar Kabir ne ya bayyana hakan lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi jim kadan bayan kammala amincewa da kasafin a Abuja.
Ya ce ɗaukar matakin ya zama wajibi la’akari da kuɗin da aka ware wa daliban a cikin kasafin ya yi kadan.
Abubakar ya kuma ce kwamitin ya kara kason da aka ware wa Ma’aikatar Tsaro daga Naira miliyan dubu 476 zuwa miliyan dubu 546 sakamakon ƙaruwar kalubalen tsaro.
Shugaban kwamitin ya kuma ce sun duba tare da amincewa da batun kara mafi ƙarancin albashin ma’aikata domin mika shi ga bangaren zartarwa.
Ya ce za su tabbatar da sa ido ga bangaren zartarwa domin ganin an yi abin da ya dace.
Sai dai kuma Fadar shugaban kasa ta ce jirgin ruwan, ba na amfanin Tinubu ba ne, na Rundunar sojojin Ruwan Najeriya ne.