Majalisar wakilan ƙasar nan ta buƙaci a ƙara inganta harkokin tsaro a filayen sauka da tashin jiragen saman ƙasar nan domin ƙara tabbatar da tsaro.
Wannan kira ya fito ne ta bakin ɗan majalisar wakilai, Jimoh Olajide, a yayin gabatar da ƙudurinsa sakamakon wata hatsaniya a yayin da wani fasinja ke ƙoƙarin hawa jirgin saman da ake kira da Ibom Air plane.
Fasinjan wanda aka bayyana sunansa da Obiajulu Uja, da kuma ya ayyana kansa a matsayin ɗan a mutum ɗan takarar jam’iyyar Labour Party, ya ta da ƙura kan cewa lallai a guji rantsar da Tinubu a matsayin shugaban ƙasa.
Wannan hatsaniya ta haifar da tsaro a zukatan sauran fasinjoji wanda ta kai ga sai da jami’an tsaro na hukumar filin sauka da tashin jiragen Nnamdi Azikiwe da ke abuja suka kawo ɗauki tare da yin awon gaba da shi.
Wannan hatsaniya da aka yi da fasinjan ta jawo dakatar da tashin jirgin fasinjojin na wani ɗan lokaci.
A jiyar Olajide, akwai buƙatar gwamnatin tarayya ta tabbatar da an samar da tsaro a filayen sauka da tashin jirage da ke faɗin ƙasar nan domin tabbatar da kwanciyar hankali a zukatan masu tafiye-tafiye
Sannan ya yi kira ga gwamnati kan ta ƙara samar da ƙarin na’urorin tsaro na zamani domin inganta tsaro a ƙasar.