A yau Laraba ne ake sa ran za a karanto sunayen mutanen da Shugaba Tinubu zai naɗa a matsayin ministoci a zauren majalisar dattawa, bayan an daɗe ana jira.
Hakan na zuwa ne bayan da shugaban ƙasar ya aike da jerin sunayen ga majalisar dattawa a jiya Talata, 18 ga watan Yuli,
Rahotanni sun nuna cewa magatakardan majalisar, Magaji Tambuwal ya karɓi wasiƙar shugaban ƙasar mai ɗauke da sunayen ministocin a jiya Talata.
Haka kuma Shugaban ƙasa Tinubu ya miƙa sunayen ministocin ga hukumomin tsaron farin kaya ta DSS da hukumar da ke yaki da masu yiwa tatttalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC domin yin binciken ƙwaƙwaf a kansu.
Wasu majiyoyi sun yi iƙirarin cewa hakan da shugaban ƙasar ya yi wata hanya ce ta tsame wasu manyan jiga-jigai waɗanda kai tsaye ba za a iya ƙin basu muƙamin minista ba.