Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United za ta buga wasanni har guda tara a cikin watan Afirilu da ya hada da na gasar Europa League da Premier da kuma kofin alubale na FA Cup.
A wasanni taran da ungiyar za ta fafata a cikin watan Afirilun za ta yi Premier League shida da Europa League biyu da FA Cup daya kuma cikin wasannin za ta buga karawa biyar a Old Trafford, sannnan ta yi hudu a waje.
Sannan a ranar Lahadi 2 ga watan Afirilu Manchester United za ta ziyarci Newacastle United a karawar Premier a filin was ana St James Park sannan cikin sauran wasannin Premier League da za ta buga, za ta karbi bauncin Brentford da Everton a Old Trafford, za ta je gidan Nottingam Forest.