Manyan hafsoshin tsaron ECOWAS za su sake yin wata ganawa ta musamman a kasar Ghana don ci gaba da tattauna yiwuwar amfani da karfin soja, a kan sojojin Nijar, musamman a yanzu da suke barzanar hallaka hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum.
An dai shirya wannan taron ne a ranar Asabar din da ta gabata, amma aka dage shi bayan da shugabannin kungiyar suka amince da fara aikewa da sojoji Jamhuriyar Nijar don tabbatar da mayar da dimokuradiyya kasar.
Har yanzu dai matsayar da ECOWAS ke dauka na ci gaba da rikitar da mutane, la’akari da yadda ta ke shan alwashin amfani da karfin soji, a wasu lokutan kuma ta ce akwai bukatar a yi amfani da tattaunawar diflomasiyya.
kawo yan yanzu dai babu wani tabbas a game da matakin da kungiyar za ta dauka, yayin da gwamnatin sojin Nijar din ke ci gaba da nade-nade da kuma kafa cikakkiyar gwamnati.
A yanzu dai Nijar na karkashin takunkuman ECOWAS da kuma wasu kasashen duniya.