Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da kashe Naira biliyan 320 da miliyan ɗari uku domin tallafa wa manyan makarantun ilimi a Nijeriya.
Babban Sakataren asusun tallafa wa manyan makarantun ilimi (TETFund), Sonny Echono, ne ya bayyana hakan jiya Laraba a Abuja, a yayin taron shekera-shekara da suke gudanarwa tare da shugabannin manyan makarantun da suke amfanuwa da tallafin.
Echono ya ce taron wata dama ce ta samun bayanai tare da auna tasirin ayyukan asusun domin ƙara inganta ayyukansa.
Shugaban TETFund ɗin ya bayyana cewa a tallafin na bana, ana sa ran kowacce Jami’a za ta samu Naira biliyan 1 da miliyan 154 da dubu 732 da 133.
Inda Makarantun kimiyya na Polytechnic za su sami Naira miliyan 699 da dubu 344 da 867.
Yayin da Kwalejojin Ilimi za su samu Naira miliyan 800 da dubu 862 da 602