Mai martaba sarkin kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya ce masarautar kano ta damu da yawan samun karuwar matasa da yan mata masu shan miyagun kwayoyi da ake samu a jihar Kano.
Mai martaba sarkin Alhaji Aminu Ado ya tabbatar da cewa masarautar kano a shirye take domin aiki da jami’an tsaro, da kungiyoyin al’umma domin kawo karshen matsalar shan miyagun kwayoyi.
A sanarwar da babban Sakataren yada labaran Masarautar Kano Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ya ce Sarkin ya bayyana haka ne a lokacin da gamayyar kungiyoyin arewacin kasar nan karkashin jagorancin Sharif Nastura wadanda suka kai masa ziyara a fadarsa.
Ya kuma shawarci matasa wajen kaucewa ta’ammali da kwayoyin duba da yadda hakan na iya yin illa ga rayuwarsu da ma al’umma bakiɗaya.
A wani ci gaban labarin kuma shugaban cibiyar yan jaridu ta kasa karkashin jagorancin Alh Mukhtar Zubair Sa’ad ta ba wa mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero takardar karramawa domin zama cikakken mamba, a kungiyar bisa kokarin da yake wajen ci gaban al’umma a kasar nan.