Matashinan da ya shaƙi iskar ‘yanci daga gidan gyaran hali da tarbiya Yunusa Ɗahiru Kura wanda ake yiwa laƙabi da Yellow, ya bayyana ƙuncin rayuwar da ya shiga a lokacin da yake ɗaure.
Matashin ya bayyana hakan ne, a ranar Lahadi a lokacin da yake tattauna wa da manema labarai a birnin Kano.
Idan ba amanta ba rundunar ƴan sanda ta ƙasa ce ta cafke Yunusa Yellow tun a shekarar 2018, bisa zargin sa da ɗauko wata matashiya mai suna Ese Oruru daga jahar Bayelsa a kudancin Nijeriya.
Sai dai Yunusa Yellow ya musanta zarge-zargen da ake yi masa , inda ya bayyana cewa juya zancen aka yi tsakaninsa da Ese Oruru.
Yellow, ya bayyana abubuwa da kuma yadda rayuwarsa ta kasance a lokacin da yake tsare.
Yanzu haka dai ya ce zai tsaya a gida domin ci gaba da taimaka wa iyayensa, tare da faranta musu rai da duk abunda za su ji daɗi.
Yunusa Yellow ya godewa lauyoyin da suka tsaya masa, musamman Barista Huwaila Muhammad Ibrahim.
Yellow ɗan asalin jahar Kano dake arewa maso yammacin Nijeriya.