Home » Ministan Yaɗa Labarai Ya Koka da Bukatar NLC da TUC

Ministan Yaɗa Labarai Ya Koka da Bukatar NLC da TUC

Kan mafi ƙarancin albashi a ƙasar nan.

by Anas Dansalma
0 comment

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya nuna damuwarsa game da buƙatar ƙungiyoyin ƙwadago biyan Naira dubu ɗari 494,000 a matsayin mafi ƙaracin albashi.

Ministan ya ce wannan buƙata za ta jefa tattalin arziƙin Najeriya a cikin wani mahuyacin halli tare da shafar walwalar ‘yan ƙasar sama da miliyan ɗari 200.

Wannan kalamai na zuwa ne cikin wani jawabi da mataimaki na musamman ga ministan kan yaɗa labarai, Rabiu Ibrahim, ya sanya wa hannu, ya ce tuni kamfanoni masu zaman kansu suka yi na’am da tayin gwamnatin tarayya na biyan Naira dubu 60 a matsayin mafi ƙarancin albashi a ƙasar nan.

Ya ce ko shakka babbu amincewa da buƙatar ƙungiyoyin ƙwadago zai tilasta gwamnati ware kusan Naira tiriliyan 9 da biliyan 5 wajen biyan albashi wanda hakan na iya shafar tattalin arziƙin ƙasar nan.

Ya ce akwai buƙatar ‘yan Najeriya su fahimci cewa shugaba Tinubu ba shi da burin ganin ‘yan ƙasar nan sun rasa ayyukansu, musamman ga waɗanda ke aiki a kamfanoni masu zaman kansu waɗanda ba lallai su iya biyan albashin da ‘yan ƙwadago ke son a biya ba.

Ya ƙara da cewa ‘yan ƙwadago sun fi mai da hankali ne kan ma’aikata kusan miliyan ɗaya da dubu ɗari biyu wanda saɓanin shugaba Tinubu da ke kallon walwalar mutane miliyan 200 da kuma kacokan tattalin arziƙin ƙasar nan.

A ƙarshe ya roƙi shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago da su dawo zaman tattaunawar da ake yi tare da amince da abin da zai iya yiwuwa dangane da mafi ƙarancin albashi.

Sannan ya ba da tabbacin cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da biyan ƙarin dubu 35 ga ma’aikatan gwamnatin tarayya har zuwa lokacin da za a cimma matsaya na mafi ƙarancin albashi a ƙasar nan.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi