Hukumar sadarwa ta Najeriya ta ce ta damu da korafe-korafen da ‘ƴan ƙasa ke cigaba da yi mata a kan yadda datarsu ta sati ko wata ko shekara ke saurin ƙarewa.
Wannan dalilin ne ya sa hukumar sadarwar ta Najeriya, ta yi yunƙurin gano dalilin da ya sa hakan ke faruwa.
A binciken da hukumar ta yi, ta gano cewar cinyewar data a waya ko na’ura mai ƙwaƙwalwa ta samo asali ne ga yadda ake samun sababbin kayan na’urori masu shan data a duk faɗin duniya.
Hukumar sadarwar ta Najeriya ta zargi masu amfani da waya da alhaƙi shanye datarsu da kansu, inda ta ce hakan yana da nasaba da kayan da suke siya sababbi masu amfani da data mai nauyi.
Hukumar ta ce, saurin sauke abubuwa zuwa kan waya da kuma saurin haɗa na’ura da yanar gizo-gizo a ɗan kankanin lokaci na da nasaba da saurin cinyewar data.
Ƙorafe-ƙorafe masu amfani da datar sun haɗa da, korafin cewa datar da suke siya ta wata ba ta yi musu wata take ƙarewa. Yayin da wasu suka ce, datar sati ba ta yi musu satin, kawai sai dai suji an cire su daga shiga yanar gizo-gizo.
Da yake bayani ga ɗimbin jama’a a taro na 91 da aka yi na “Majalisar Masu Amfani da Waya mai taken “Zuƙewar Data” Mataimakin shugaban hukumar sadarwa na ƙasa, Farfesa Umar Garba Danbatta yace:
Masu amfani da Data suna fuskantar zuƙewar data, kuma suna musu ƙorafi.
Ya ci gaba da cewa: “Illar da aka samu ta Cutar korona ita ce babbar jigo a cikin matsalar, domin ta haifar da samuwar sababbin ababen kimiyya da fasaha.