Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa’ad III ya sanar da ganin jinjirin watan Shawwal a Najeriya.
Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar III ya ce ganin jinjirin watan da aka yi a a kasar ya sanya ranar Juma’a 21 ga watan Afrilu, 2023 ta zamo 1 ga watan Shawwal, 1444.
Kwamitin tantance ganin wata karkashin jagorancin Maigirma Wazirin Sakkwato Farfesa, Sambo Wali Junaidu ne ya jagoranci aikin tabbatar da ganin watan.
Domin haka Sarkin Musulmi ya tabbatar da gobe Juma’a a matsayin ranar sallah ƙarama