Aljeriya ta ce mutum 15 ne suka mutu sakamakon ɓarkewar gobarar daji yayin da ake ci gaba da fuskantar tsananin zafi.
Mutanen sun mutu ne a lardunan Bejala da Bouria da ke kan tsaunuka, inda masu kashe gobara sama da 7,000 ke can suna ƙoƙarin shawo kan wutar.
Zuwa yanzu, an kwashe mutane sama da 1,500 daga yankin.
Hukumar lura da yanayi ta ƙasar ta yi gargaɗin cewa za a ci gaba da samun yanayi da zai kai maki 48 na ma’unin celsius har zuwa karshen wata a yankin arewacin ƙasar.
Hakan ya biyo bayan fuskantar tsananin zafi a faɗin Afrika – wanda ya kai maki 50 a wasu yankuna.
Rahotanni sun bayyana cewa buƙatar wutar lantarki a cikin mutanen Aljeriya ya kai kololuwar da ba a taɓa ganin irinsa ba a tarihi, tun da aka fara smaun tsananin zafi.