Mahukunta sun tabbatar da mutuwar mutane 85 cikin kwanaki da aka kwashe ana rikici tsakanin makiyaya da manoma a jihar Filato da ke Arewa Maso Tsakiyar ƙasar nan.
Rikicin ya ɓarke ne tun a ranar Litinin a yankin da ake yawaita samun rikicin ƙabilanci da addini a tsawon shekaru.
Har yanzu dai babu wasu sahihan bayanai da ke tabbatar da ainihin abin da ya hadasa rikicin.
Irin wannan rikici tsakanin makiyaya da manoma domin ɗaukar fansa abu ne da aka saba gani a kauyuka da dama da ake fama da hare-haren ‘yan bindiga.
Hukumar agajin gaggawa ta jihar wato SEMA ta ce rikicin ya raba dubban mutane da muhallasu.