Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa mutane sama da dubu dari takwas ka iya tserewa daga Sudan sakamon kazamin fadan da ake yi tsakanin bangarorin soji biyu da ke gaba da juna.
Ana ci gaba da gwabza fada a babban birnin kasar, wato Khartoum duk da alkawarin dakatar da bude wuta tsakanin bangarorin biyu.
Tuni dubban ‘yan kasar da ma kasashen waje suka fice daga kasar ta gabashin Afirka.
Kazamin fadan wanda ya barke tun sama da mako biyu da ya gabata
Tuni ya haifar da kwararar dubban ‘yan kasar ta Sudan zuwa kasashe makwabta da suka hada da Masar da Chadi da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka.
Haka su ma ‘yan kasashen waje gwamnatocin kasashensu da sauran hukumomi na ci gaba da kokarin kwashe su daga kasar, inda tuni suma dubbai suka fice.