Matsalar mace-macen mata da yara a lokacin rainon ciki ko haihuwa dai ta jima ta na ci wa ƙasashe masu tasowa tuwo a ƙwarya.
Alal misali, ƙasashen da suka ci gaba mata 7 zuwa 15 ne ke mutuwa a cikin mata masu juna 100,000 daga lalurar ciki ko haihuwa;
Amma a ƙasashe masu tasowa har wajen mata 100-300 ne kan rasu sanadiyyar lalurorin ciki ko haihuwa.
Wani sabon rahoton da hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya suka fitar na cewa a duk minti biyu mace na mutuwa a duniya yayin da take ɗauke da juna biyu ko haihuwa.
Hakan na ƙara nuna rashin kyawun yanayin kula da mata masu juna biyu a yankin kudu da hamadar sahara, wanda ke haddasa mafi yawan mace-macen.
A shekara ta 2004, Hukumar Lafiya ta Duniya ta ayyana mace-macen mata masu juna biyu a matsayin mutuwar da ke da alaƙa da juna biyu a lokacin ɗaukar ciki ko kuma cikin kwanaki 42 na ciki, wanda aka bayyana a matsayin rabon haihuwar 100,000 a cikin al’ummar da ake nazari.
Rahoton, ‘Trends in Maternal Mutality 2000-2020,’ wanda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), da Asusun Kula da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF), da Asusun Kula da Al’umma ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNFPA), da Rukunin Bankin Duniya da Sashen Majalisar Ɗinkin Duniya suka gabatar da Cibiyar Tattalin Arziki da Harkokin Jama’a (UNDESA), ta nuna raguwar lafiyar mata a ‘yan shekarun nan.
Rahoton ya kuma bayyana cewa kashi 70 cikin 100 na mace-macen mata masu juna biyu a shekarar 2020 an samu ne a yankin kudu da hamadar Sahara.
A duk duniya, rahoton ya nuna cewa an samu mace-macen mata masu juna biyu kusan 287,000 a shekarar 2020. Wannan ya nuna an samu raguwa kaɗan daga 309,000 a shekarar 2016, bayan ƙaddamar da muradun ci gaba mai ɗorewa na Majalisar Dinkin Duniya (SDG).
A cewar WHO, an kiyasta cewa a yankin kudu da hamadar sahara, mata 390 ne za su iya rasa ransu a lokacin haihuwa a kowace mace 100,000 da suka haihu nan da shekara ta 2030.
Abin baƙin ciki ne dai yadda mata da yawa a Nijeriya ke mutuwa yayin da suke da juna biyu da haihuwa duk da dimbin arzikin da muke da shi na ɗan Adam da abin duniya.