Gwamnan jihar Neja, Umar Bago ya ce gwamnatinsa tana sa ran samun Naira tiriliyan ɗaya na kudin shiga da za a samu daga Kanfanin Samar da Abinci da Sufuri na Jihar a cikin shekaru biyar masu zuwa.
Mashawarci na musamman ga gwamnan kan kafafen yaɗa labarai na zamani, Abdullberqy Ebbo, ne ya bayyana a hakan a ciki wata sanarwa da ya fitar a jiya a Abuja.
A cewarsa, wannan shiri da gwamnati ke yi, zai samar wa da manoma dubu 100 aikin yi waɗanda ake sa ran za su noma kusan hekta dubu 100 a fadin jihar.
Ya ce tuni aka ƙulla yarjejeniya tsakanin shugaban kanfanin samar da abincin na jihar Neja, Sammy Adigun, da kuma babban daraktan kanfanin TGI, Sadik Kassim.
Kuma a ƙarƙashin yarjejeniyar, gwamnatin jihar da kuma kanfanin samar da abincin za su ɗauki alhakin noma, da girbi da sayar da abubuwan da za a noma da suka haɗa da shinkafa da waken suya da masara da riɗi ga kanfanin na TGI.
Kuma za a tabbatar da an samar da sama da tan dubu ɗari shida na kayan amfanin goma a cikin tsawon shekarun biyar masu zuwa.