Wani kamfanin Najeriya mai suna EGTA Investment Limited, ya ƙulla yarjejeniya da wani rukunin kamfanonin ƙasar Ghana da ake kira Jospong Group of Companies, da nufin haɓaka noma.
Yarjejeniyar wadda ɓangarorin biyu suka rattaba wa hannu a ofishin jakadancin ƙasar Ghana da ke birnin Abuja, za ta bada ƙarfi ne kan bunƙasa noman shinkafa, da alkama, da waken soya, da masara, da ƴaƴan biye rana da kuma sauran wasu albarkatun.
An rattaba wa yarjejeniyar hannu ne akan idon ƙaramin ministan albarkatun ruwa da tsaftar muhalli na Najeriya, Alhaji Bello Goronyo da Mataimakin jakadan ƙasar Ghana Mista Eddison Agbenyegah da kuma Aminu Goronyo, shugaban ƙungiyar manoman shinkafa ta Najeriya RIFAN.
Shugaban kamfanin EGTA Mista Bashir Ibrahim ya ce yarjejeniyar da aka ƙulla tana da mahimmaci wajen samar da masu zuba jari a harkokin noma. Haka kuma ya ce akwai buƙatar hannun jarin da ya dace don samun cigaba a fannin bunƙasa noma a Afirka ta hanyar haɗa gwiwa da yin hulɗar da ta shafi hada-hadar kuɗi, da zamantakewa da kuma siyasa tsakanin ƙasashen Afirka.
Ibrahim yace wannan haɗin gwiwa tsakanin kamfanonin biyu tamkar wani ci gaba ne na tarihin hulɗar da ke tsakanin Najeriya da Ghana, yace yarjejeniyar za ta kula da noman kayan abinci, kuma za ta samar da haɗin gwiwa ta ɓangaren fasaha da hada-hadar kuɗi da zuba jari, da kuma taimaka wa juna da dabarun aiki ta hanyar horaswa da yin bita don ƙarfafa yanayin noma a ƙasar Ghana.
Shi ma Mista George Blavo babban mai kula da tsare-tsare a ɓangaren noman shinkafa a rukunin kamfanonin Jospong na ƙasar Ghana, wanda kuma shi ne ya rattaba wa yarjejeniyar hannu da sunan rukunin kamfanonin, ya ce yarjejeniyar ta dace da manufofin ƙasar Ghana na bunƙasa aikin noma. Blavo yace an ƙulla yarjejeniyar ne takanas da nufin raba al’ummar ƙasar Ghana da fatara ta hanyar haɓaka aikin noma.
A nasa ɓangare Mataimakin jakadan ƙasar Ghana Mista Eddison Agbenyegah ya ce Ghana tana so ne ta yi koyi da Najeriya wadda tun ba yau ba ta yi fice a noman shinkafa, kuma a nahiyar Afirka tana gaba-gaba a harkar noman na shinkafa.