Home » Najeriya Na Shirin Kwaso Ɗalibanta Karo Na Biyu Daga Ƙasar Sudan

Najeriya Na Shirin Kwaso Ɗalibanta Karo Na Biyu Daga Ƙasar Sudan

by Anas Dansalma
0 comment
Najeriya Na Shirin Kwaso Ɗalibanta Karo Na Biyu Daga Ƙasar Sudan

A yayin da ake shirin fara kwaso rukunin na biyu na ɗaliban ƙasar nan da ke Sudan, rahotanni na cewa rukunin farko da aka kwaso bas u samu damar shiga ƙasar Masar ba,  bayan da hukumomin kasar suka hana rukunin shiga kasar ba tare da takardun biza ba.

Hukumar da ke kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen ketare NIDCOM, ta ce a ranar Asabar za ta kwaso rukuni na biyu na ‘yan Najeriya da yakin Sudan ya rutsa da su.

Mafi aksarin ‘yan Najeriya da suka makale a Sudan dalibai ne.

“Ofishin Jakadancin Najeriya a Sudan na mai sanar da dukkan ‘yan Najeriya da ke bukatar a kwashe su cewa a ranar 29 (Asabar) ga watan Afirlun 2023, ofishin jakadancin zai fara kwasar jama’a a karo na biyu zuwa Masar, inda daga can za a dauke su a jirgin sama zuwa Najeriya.

“Duk wanda yake da bukatar tafiya, ya zo Jami’ar Al Razi (Al Azhari) da ke titin Madani da safe. Ba a so mutum ya ruko sama da jaka daya.” In ji wata sanarwa da NIDCOM ta fitar dauke da sa hannun jakadan Najeriya a Sudan, H.Y. Garko a shafin Twitter a ranar Juma’a.

A farkon makon nan Najeriya ta kwaso rukunin farko inda aka nufi kasar Masar da su.

Sai dai rahotanni na cewa, rukunin farko da aka kwaso ya makale a kan iyakar Masar, bayan da hukumomin kasar suka hana shi shiga kasar ba tare da takardun biza ba.

Bayanai sun yi nuni da cewa, akwai akalla mutum 7,000 daga kasashe daban-daban cikinsu har da ‘yan Najeriya, da suka makale akan iyakar suna neman a bar su su shiga Masar.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?