Tsohon shugaban ya bayyana hakan a wurin wani taro a jihar Legas, inda ya koka da yadda rashin tsaro a ƙasar nan ke ci gaba da jefa mutane cikin fargaba da yunwa.
Domin magance wannan matsala, Obasanjo ya ce akwai buƙatar kyakkyawan jagoranci da ai inganta rayuwar al’umma.
Ya ce za a iya samar da kyakkyawan shugabanci ne kaɗai idan aka samu sabbin jagorori masu tsoron Allah da son kawo canji da kuma jin cewa al’umma za su bautawa.
Sannan ya ce duk yawan arziƙin da muke taƙama da shi ba zai kai mu ko’ina ba, idan aka ce babu kyakkawan shugabanci a ƙasar nan wanda ya ce hakan ne ya sa shugabanci ya zama muhimmin abun damuwa a Afirka.