Gwamnatin Najeriya ta ce ya kamata a aiwatar da tsarin samar da kasashe biyu masu cin gashin kansu wato kasar Falasdinawa da ta Isra’ila don a tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a yankin Gabas Ta Tsakiya.
Ministan Harkokin Wajen Najeriya Yusuf Maitama Tuggar ya ce rikicin ya jefa mutanen da ba su ji ba su gani ba cikin mawuyacin hali, yana mai kira ga Isra’ila ta bari a shiga Gaza da kayan agajin jinkai. Ministan ya jaddada kira a yi gaggawar tsagaita wuta a yakin Isra’ila da Falasdinawa
Ya ce dole ne bangarorin biyu su kiyaye ‘yancin dan Adam da kuma dokokin jinkai na kasashen duniya wadanda suka bukaci a kare lafiyar fararen-hula a yayin da ake rikici.