Home » NDLEA ta damke wasu mutane 4 da ke safarar miyagun kwayoyi a Najeriya

NDLEA ta damke wasu mutane 4 da ke safarar miyagun kwayoyi a Najeriya

by Anas Dansalma
0 comment
NDLEA ta damke wasu mutane 4 da ke safarar miyagun kwayoyi a Najeriya

Jami’an hukumar hana sha da fataucuin miyagun kwayoyi wato NDLEA  sun damke wasu mutane hudu da ake zargi su na da hannu a harkar safarar miyagun kwayoyi a Najeriya.

Wani  rahoton na nuni da cewa , an fahimci cewa wadanda su ka shiga hannun ma’aikatan na NDLEA sun hada da ma’aikatan coci.

Har ila yau akwai ma’aikaciyar wani kamfani da wata mata dabam da ake tunani su na taimakawa wajen yawo da mugayen kwayoyi a jihar Delta.

Ana haka kuma rahoto ya zo cewa jami’an hukumar sun auka wani kamfani da ke garin Ogun, su ka kuma yi nasarar cafke kilo 4,560 na kwaya.

Hukumar ta NDLEA ta cafke miyagun kwayoyi ne a garuruwan Legas, Adamawa da kuma Osun.

Mai magana da yawun bakin hukumar yaki da ciniki da fataucin kwayoyin kasar, Femi Babafemi ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar a yau .

 Jawabin da aka fitar a Abuja ya ce an cafke ‘yan kwayan fentanyl da ke aiki a Warri ta jihar Delta, wata guda bayan kama wasu mutane a jihar Anambra.

Femi Babafemi ya ce sun iya kama wadanda ake zargi ne bayan tsawon lokaci ana binciken shigowar wata kwaya da ta fi Heroine hadari a Duniya.

Ma’aikatan da aka kama su na aiki ne a cocin Christ Mercyland Deliverance Ministries wanda aka fi sani da cocin Mercy City Church a Warri.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?