Shugaban hukumar hana sha da fataucin muggan kwayoyi (NDLEA), Janar Buba Marwa mai ritaya ya tabatar da cewa tsauraren matakan da suke dauka kan yaki da ta’ammuli da muggan kwayoyi ya haifar da Ɗa mai ido, domin a cikin watani 29 kacal hukumar ta damke masu ta’ammuli da muyagun kwayoyi su 31,675.
Hukumar ta NDLEA ta kara da cewa cikin 31,675 da aka kama, 5,147 an tabbatar da laifinsu kuma an yanke masu hukunci, yayin da hukumar ta kwace muggan kwayoyi da suke da nauyin miliyan 6.3 a tsawon wannan lokaci.
Ya kara da cewa wannan kokarin yana cikin hobbasan da hukumar ke yi don hana jama’a ta’ammuli miyagun kwayoyi wanda a yanzu ya zama ruwan dare a tsakanin al’umma kuma yana barzana ga ci gaban tattalin arziki da su kansu masu amfani da kwayoyin da kuma iyalansu.