Home » NGO: An kaddamar da kundi kan yaƙi da safarar bil’adama a Najeriya

NGO: An kaddamar da kundi kan yaƙi da safarar bil’adama a Najeriya

by Muhammad Auwal Suleiman
1 comment
NGO: An kaddamar da kundi kan yaƙi safarar bil’adama a Najeriya

Wata ƙungiya mai zaman kanta, ta yi kira ga masu ruwa da tsaƙi da malaman addini a Najeriya da su sa hannu kan yaƙin da ake yi wajen kawo ƙarshen safarar bil’adama a ƙasar nan.

Wannan kira na zuwa ne a yayin wani taro na wuni ɗaya na ƙaddamar da kundi na Cibiyar Addinai ta ƙasa kan daƙile safarar bil’adama a Najeriya.

Taron dai an ba shi taken: YAƘI DA SAFARAR BIL’ADAMA TA HAƊAKAR  ADDINAI.

A cewar daraktan ƙungiyar Gamayyar Yaƙi da Safarar Bil’adama da Ba da Taimaka ta MECAHT, wannan taro zai ƙara jaddada haɗin kan da ake da shi wajen yaƙi da wannan mummunar ɗabi’a.

Shi ma a nasa jawabin, shugaban ƙungiya mai zaman kanta ta ba da agaji ga masu rauni da ƙananan yara da waɗanda suka gamu da ibtila’i ta SURE4U kuma tsohon shugaban hukumar shigi da fici ta Najeriya, Muhammad Babandede, ya ce abu ne mai kyau shigo da malaman addini cikin wannan yaƙi da ake yi zai taimaka wajen kawo ƙarshen safarar bil’adama a Najeriya.

Ya ce kundin da suka gabatar zai taimaka wa jami’an tsaro da masu zartar da hukunci da masu ba da tallafi da kafafen yaɗa labarai da sauran masu ruwa da tsaƙi  wajen yaƙi da safarar bil’adama.

Ya ƙara da cewa abu ne mai muhimmanci limamai na addinin musulunci da na mabiya addinin Kiristanci da su samu wannan kundi da ake yi bayanin matakan da ya kamata a ɗauka game da wannan matsala.

Ya ce yana da kyau kuma a samar da wani kundin makamancin wannan ga ‘yan siyasa da masu riƙe da muƙamai a ƙasar nan domin cusa musu tausayin talakawa domin hakan zai taimaka wajen yaƙi da safarar bil’adama a Najeriya.

You may also like

1 comment

Salisu Muhammad auwal hadejia December 21, 2023 - 12:06 am

Slm ni sunana salisu Muhammad auwal Kuma Mai Girma Muhammad babandede Yamin komai saidai Allah ya sakamasa da alkairi saboda Shi yasamin karsahin makaranta araina day Sana saboda nayi aiki a gonarsa tsawon shekara hudu Kuma yabani kudin da nayi rigistarashin Kuma Kuma ta aikin da nake agonarsa ne nake temakon iyayena da kannena Allah yaji kan iyeye day kakanni

Reply

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?