Nijeriya ta jaddada aniyarta ta cigaba da zama mamba ta kungiyar ƙasashen masu arziƙin man fetur, OPEC, inda karamin ministan man fetur Heineken Lokpobiri ya ba da tabbacin cewa ƙasarsa ba za ta gaza ba wajen ci-gaban kungiyar.
Ya ce hadin kan kungiyar shi ne yake samar da zaman lafiya da dorewar cinikayya a kasuwar man fetur.
Don haka, ya ce za su tsaye tsayin-daka wajen ganin OPEC ta cim ma muradunta tare da magance duk wani ƙalubale da ya shafi kasar nan da ma nahiyarmu bakiɗaya.
Ita ma ƙasar Kongo ta jaddada aniyarta ta cigaba da kasancewa mamba a kungiyar bayan kwanaki kadan da makwabciyarta Angola ta yanke shawarar fita daga kungiyar.
An bai wa Kongo, wadda ta zama cikakkiyar mamba ta OPEC a 2018, damar fitar da ganga 277,000 na danyen fetur a kullum zuwa 2024, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.