Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar a fuskanci tsananin zafin rana a faɗin wasu jihohin ƙasar nan.
A cewar hukumar, mutane na gab da fara jin sauyi, inda za a riƙa tsala ranar mai zafin gaske.
Jihohin da aka yi hasashen za su fuskanci ƙaruwar zafin ranar sun haɗa da: Kebbi da Sokoto da Zamfara da Taraba da Adamawa da Oyo da Kwara.
Sai kuma birnin Tarayya Abuja da Nasarawa da Benue da Bauchi da Gombe da kuma Borno.
Hukumar ta kuma bayyana cewa zafin ranar zai kai mizanin maki 40 a ma’aunin selsiyos a cikin kwanaki biyu masu zuwa.
Nimet ta ce jihohin da makin zai haura 40 sun haɗa da wasu sassan Sokoto da Kebbi da Zamfara da Taraba da kuma Adamawa.
Hukumar ta sharwarci mutane da ke zaune a jihohin da abin zai shafa da su riƙa shan isasshen ruwa a tsawon lokacin.
Tare da shawartar masu azumi da kar su riƙa fita cikin ranar, su kuma riƙa shan wadataccen ruwa a lokatan shan ruwa da sahur.