Home » NNPP a Kano Ta Yi Alƙawarin Bin Kadin Zaɓukan Wasu ‘Yan Majalisu

NNPP a Kano Ta Yi Alƙawarin Bin Kadin Zaɓukan Wasu ‘Yan Majalisu

by Anas Dansalma
0 comment

Umar Haruna Doguwa wanda shi ne shugaban jam’iyyar a jihar Kano, ya ce “Akwai abubuwa da dama da suka faru waɗanda ba mu gamsu da su ba, waɗanda kamar an mayar da hannun agogo baya ne.

yi zargin cewa an tayar da hankula a wurare da dama a lokacin zaben da aka kammala.

Ya kuma ce za su yi nazari tare da neman hanyar da za a bi wa ƴaƴan jam’iyyar na NNPP hakkinsu.

Jam’iyyar ta ce ba ta yarda da sakamakon ba ne kasancewar tana zargin cewa an tafka magudi a wasu wuraren da aka yi zaben.

Jihar Kano ce ke da ƴan majalisu mafi yawa na jiha wadanda zaɓen su bai kammala ba a zaben 18 ga watan Maris 2023, inda aka kammala zaben a ranar Asabar 15 ga watan Afrilu, kuma aka an sanar da sakamako.

A sakamakon da INEC ta bayyana, jam’iyyar APC ta lashe mazabar dan majalisar wakilai na Tudun Wada da Doguwa, yayin da NNPP kuma ta samu nasara a karamar hukumar Fagge.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?