• Home  
  • NOA Ta Bukaci Dalibai Su Ci Gaba Da Martaba Nijeriya Da Al’adunsu.
- Babban Labari - Labarai

NOA Ta Bukaci Dalibai Su Ci Gaba Da Martaba Nijeriya Da Al’adunsu.

Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa, NOA, ta bukaci yara da dalibai su kasance masu nuna kishin kasar su da bin doka don zama wadanda za a yi alfahari da su anan gaba. Darakta Janar, na jukumar NOA Mallam Lanre Issa-Onilu, ya bayyana hakan lokacin da ya karɓi baƙuncin ɗaliban makarantun, CK Academy, Bmuko […]

Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa, NOA, ta bukaci yara da dalibai su kasance masu nuna kishin kasar su da bin doka don zama wadanda za a yi alfahari da su anan gaba.

Darakta Janar, na jukumar NOA Mallam Lanre Issa-Onilu, ya bayyana hakan lokacin da ya karɓi baƙuncin ɗaliban makarantun, CK Academy, Bmuko Dutse, da kuma Goldsworth Resource Development Academy, a zaman tattaunawar da suka gudanar a hedikwatar hukumar dake birnin tarayya Abuja.

Ya gabatar wa yaran da Dokoki Bakwai na Ɗan Ƙasa Nagari, tare da bayyana muhimmancin bin su domin gina Najeriya ta gari.

Ya kara da cewa hukumarNOA, za ta ci gaba da wayar da kan jama’a ta hanyar shirye-shieyen da gwamnati ta ke shiryawa don samun hadin kan kasa

A nata jawabin, Mrs Cynthia Opene wadda ke gabatar da shirin yara na Kiddies World a NTA Channel 5, ta yaba da tarbar da NOA ta yi, tana mai cewa ziyarar ta nuna irin rawar da hukumar ke takawa wajen inganta tarbiyyar yara.

A karshe Mallam Lanre Issa-Onilu ya yara sune manyan gobe don haka su zamo masu nuna kyakkyawar halayya a duk inda suka samu kansu don a yi alfahari dasu anan gaba.

Game Da Mu

Gidan Radio da talabijin mai kawo muku labarai akan rukunoni daban daban. Da Hausa Muke Magana.

Yi Mana Imel: info@muhasatvr.ng

Tuntuɓi: +(234) 912 222 1000