Home » PDP Ta Gabatar da Wasu Shaidu a Zaman Sauraron Kararrakin Zaben Shugaban Kasa

PDP Ta Gabatar da Wasu Shaidu a Zaman Sauraron Kararrakin Zaben Shugaban Kasa

by Muhammad Auwal Suleiman
0 comment
PDP Ta Gabatar da Wasu Shaidu a Zaman Sauraron Kararrakin Zaben Shugaban Kasa

Dan takarar shugabancin kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya gabatar da wasu shaidu a gaban kotun sauraron korafe-korafen zabe da ke zamanta a Abuja.

Kotun sauraran korafe-korafen zabe a Abuja ta amince da shaidar da dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya gabatar.

Kotun ta karbi wannan takardun ne a jiya Juma’a 23 ga watan Yuni da suka hada da takardar shaidar bautar kasa da na kammala digiri da kuma takardar shaidar aiki na kamfanin Mobil Oil Nigeria Plc.

Jam’iyyar PDP ta gabatar da shaidar ta hannun Mike Enahoro Ebah wanda ya ce takardun Tinubu ne ya karbe su amma suna dauke da sunan Bola Adekunle Tinubu.

Jagoran lauyoyin PDP, Chris Uche ya ce mai ba da shaidan ya kuma gabatar da wasu takardu da kuma wasika zuwa ga hukumar zabe, cewar lauyan hukumar zabe, Abubakar Mahmud da lauyan Tinubu, Emmanuel Ukala da kuma lauyan APC, Lateef Fagbemi dukkansu sun ki yarda da wadannan shaidun da PDP ta kawo.

Atiku da jam’iyyar PDP sun shigar kara kan zargin magudin zabe da aka tafka a zaben da ya gabata.

Peter Obi da Atiku Abubakar na kalubalantar babban zaben da aka gudanar a watan Faburairu na shugaban kasa a Najeriya

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?