Home » PDP Ta Kori Nyeson Wike

PDP Ta Kori Nyeson Wike

Babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP ta sanar da korar ministan Abuja, Nyesom Wike, da wasu jiga-jiga daga cikinta, saboda abin da ta kira yi wa jam

by Mujahid Wada Guringawa
0 comment

Babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya, PDP ta sanar da korar ministan Abuja, Nyesom Wike, da wasu jiga-jiga daga cikinta, saboda abin da ta kira yi wa jam’iyya zagon-ƙasa.

Cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce ta ɗauki matakin ne domin kawo haɗin kai da ladabtarwa a jam’iyyar da kuma mayar da hankali ga zaɓukan 2027 masu zuwa.

Sauran mutanen da jam’iyyar ta kora sun haɗar da Samuel Anyanwu da Kamaldeen Ajibade da Ayo Fayose da Austin Nwachukwu da kuma wasu.

Sanarwar ta ce matakin ya samu amincewar mafiya rinjayen wakilan jam’iyyar da ke halartar babban taronta na ƙasa da ke gudana a birnin Ibadan na jihar Oyo.

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai mai cikakkiyar rajista wadda manufarta ita ce ilimantarwa, da wayar da kai da Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.
Muna nan a kan titin Guda Abdullahi gida mai lamba 19 a Farm Centre, jihar Kano.

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi

©MuhasaTVR 2023. Ku nemi izini kafin yin amfani da duk abin da aka wallafa a wannan shafi

Are you sure want to unlock this post?
Unlock left : 0
Are you sure want to cancel subscription?