Home » Ramadan: Shugaba Buhari Ya Gargaɗi ‘Yan Kasuwa Kan Ƙara Farashin Abin Ci

Ramadan: Shugaba Buhari Ya Gargaɗi ‘Yan Kasuwa Kan Ƙara Farashin Abin Ci

by Anas Dansalma
0 comment

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gargadi ’yan kasuwar da suke kara farashin kayayyaki saboda zuwan azumi da su daina saboda ya saba da koyarwar Musulunci.

Ya bayyana haka ne, a cikin sakonsa ga al’ummar Musulmi kan shigowar watan Ramadan da aka fara azumtar a yau Alhamis.

Shugaba Buhari, ya kuma shawarci Musulman ƙasar nan da su yi amfani da lokacin wajen haskaka kyawawan dabi’un addinin Musulunci a mu’amalolinsu, ba wai kawai a baki ba.

Sanarwar, wacce Kakakin Shugaban kasar, Malam Garba Shehu ya fitar, ta ce, “Ya kamata mu yi amfani da wannan lokacin wajen bayyana kyawawan dabi’un Musulunci irin su tausayi da kaunar juna.

Inda ya kara da cewar; “Wannan lokaci ne na komawa ga Allah da kuma jin tsoronSa, ta hanyar guje wa duk abin da zai cutar da dan Adam”.

Daga nan shugaban ya bayyana cewar  yana sane da yadda wasu ’yan kasuwa ke kara farashin kayayyaki, ciki har da na kayan abinci, a kowanne watan Ramadan. Wanda Yin hakan ya saba da ainihin manufar azumin da ma ta Musulunci,”

You may also like

Leave a Comment

Muhasa TVR kafa ce ta labarai dake da cikakkiyar rejista da ke da manufa ta ilimantarwa, wayar da kai Inganta al’adun Hausawa da kuma nishaɗantarwa.

Ofishinmu yana nan a kan titin Guda Abdullahi dake Farm Centre a jihar Kano. 

Ra'ayi

Labarai da Dumi-dumi