Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya ce rashin tsaro da Najeriya ta yi fama da shi lokacin mulkinsa, daga 2010 zuwa 2015 shi ne abin da ya fi tayar masa da hankali a tsawon shugabancinsa.
Wata majiya ta ruwaito cewa Jonathan ya bayyana haka ne a yayin kaddamar da aikin titin Yola-Wukari mai tsawon kilomita 22 a jihar Taraba.
Da yake yaba wa Gwamna Darius Ishaku kan abin da ya bayyana a matsayin aiki na gari da ya yi, tsohon shugaban ya bayyana cewa mafi munin mafarkinsa a matsayinsa na shugaban ƙasa shi ne rashin tsaro.
Ya ce ya kasance ba ya barci a yawan lokuta saboda ganin ya laluɓo hanyar warware matsalolin tare da karfafa wa mazauna yankin gwiwa da su zauna lafiya domin samun ƙarin ci gaba.
Ya kara da cewa ababen more rayuwa kamar tituna su ne jigon duk wani ci gaba.
Da yake kaddamar da aikin titin, Jonathan ya ce tsaro yana hannun jama’a ne.