Shugaban rundunar sojin sama ta Najeriya, Air Marshal Hassan Abubakar, ya ba da tabbacin cewa Najeriya na sa ran isowar jirage masu saukar ungulu har 18 domin inganta ayyukan rundunar.
Ya bayyana hakan ne a garin Fatakwal a yayin da ya kai ziyara reshen rundunar sojin sama ta musamman dake jihar.
Sannan ya yi ƙarin haske kan cewa ana sa ran isowar jiragen yaƙi ƙirar AH1 Zulu Cobra guda12, ne daga ƙasar Amurka, da kuma ƙarin wasu ƙirar T129 guda shida daga ƙasar Turkiyya a cikin watan Satumba.
Shugaban ya kuma tabbtar da cewa kai wa jirginsu hari da aka yi a jihar Neja ba zai sare wa rundunar guiwa ba.
Inda ya ba da tabbacin cewa rundunar na ƙoƙarin samar da hanyoyin magance haɗarin jiragenta da ake samu a ƙasar nan.
Cikin matakan da rundunar ke ƙoƙarin samarwa akwai yunƙurin kafa kwamitin bincike da game da dalilai da ke haifar da faɗuwar jiragen runduanr da kuma hanyoyin magance hakan a nan gaba.
Ya kuma tabbatar da cewa tuni ya ziyarci iyalan jami’an sojin rundunar da suka suka rasa rayukansu a haɗarin jirgin da ya faru a Jihar Neja da kuma jajanta musu.